(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kisan Kolade Johnson abin baƙin ciki ne ƙwarai da gaske – Shugaba Buhari

Karatun minti 1

Ana ta cigaba da alhinin kisan Mr Kolade Johnson, dan jihar Legas da hukumar ‘yan sandan RSARS ta kashe a makon da muke ciki.

Shima shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna nashi rashin jin dadin kisan Mr Johnson da akayi, har ma ya kira al’amarin da “Abin baƙin ciki  ƙwarai da gaske.”

 

“Danyen aikin da bangaren SARS na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, wanda yayi sanadiyyar mutuwar Me Kolade Johnson, abin bakin cike ne kwarai da gaske.”- Shugaba Buhari

Sai dai al’ummar kasar musamman daga yankin arewa, na ganin bakin shugaban inda yayi burus da tashe-tashen hankulan da ake ta fama dasu a yankunan Zamfara, Katsina da Kaduna’ inda ba’a taba jin shugaba Buhari ko wani babban jami’in gwamnati ya fito don nuna alhini abubuwan da suke faruwa a yankin.

Tini dai mutanen Arewa suka fara tsoma baki akan batun, inda suke cewa shugaban ya fifita wani bangare akan wasu.

A cikin makwannan, kimanin mutun 42 ne suka rasa rayukansu bisa harbin kan mai uwa da wabi da wasu ‘yan bindiga sukayi a karamar hukumar Shinkafin jihar Zamfara.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog