(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Tsaro: ‘Yan bindiga sun harbe manoma 10 a Zamfara

Karatun minti 1

Manoma guda 10 sunyi asarar rayukansu a kauyen Kursara dake unguwar Kware a karamar hukumar Shinkafin jihar Zamafara a jiya Asabar.

Manoman dai sun rasa ran nasu ne dai dai lokacin da ‘yan bindiga suka kawo hari  unguwar ta Kware.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wani mazaunin garin na Kware, ya bayyanawa wakilanta cewa, ‘yan bindigar sun shigo garin a kan babura, suka durfafo manoman a dai dai lokacin da suke aiki a gonar su ta albasa.

Ya kara da cewa, manoman sunyi yunkurin tserewa, sai dai basu samu damar yin hakan ba har suka rasu rayukan nasu.

A kwanakin nan dai garin na Kware yasha fama da irin wadannan hare-haren na ‘yan bindiga. Bisa kidudduga, a kalla mutane 62 ne suka rasa rayukansu daga watan Fabarairu zuwa watan Maris da muke ciki.

Mai magana da yawun rundunar shiyyar jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya bayyana faruwar al’amarin ya kuma bada tabbacin cewa tuni rundunar da aika jami’anta domin kwantar da tarzomar.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog