Kiwon Lafiya

Kiwon Lafiya: Mata suna gane namiji mai karyar Ido na ganin Ido – Binciken Kwakwalwar

Wata shiyar Karatun Pharmacy na Pharm D, dake kasar Pakistan, tayi wani bincike akan kwakwalan mata da maza.

Binciken ya nuna wasu abubuwa da kwakwalan mata suka fi na maza, haka suma na mazan suka fi na matan a wani kaulin.

Ga jerin Binciken:

1. Yanayin aikace-aikace (Yin Aiki dayawa lokaci guda):

Mata: Kwakwalwar mata tana da karfin bada hankalinta akan abubuwa dayawa. Mata sukan iya “Kallon Talbiji a yayin da suke waya kuma suyi girki duk lokaci daya.”

Maza: Bisa tsarin kwakwalwar maza, tana mai da hankali ne akan abu guda daya a lokaci guda. Maza suna tsayar da Talbiji a lokacin da suke waya. Ma’ana bazasu iya yi lokaci guda ba.

2. Koyar Magana/ Iya sabon Yare:

Mata: Su na iya koyan yarurruka dayawa cikin ‘dan karamin lokaci. Saidai basa iya warware matsala a cikin sauki.

“Mata suna riga maza fara yin magana a lokacin da suke kanana. Mafi yawan lokaci yarinyar ‘yar shekara 3 tafi yaron shekarar uku magana da kuma sanin kalmomin yaren da suke yi.”

Maza: Maza basa iya yarurruka dayawa a cikin kankanin lokacin, hakan ya basu wuya. Saidai sukan shawo kan matsala cikin kankanin lokaci.

3. Yin Karya

Mafi yawan lokaci, mata sukan gane maza idan sukayi musu karyar ido na ganin ido, saboda kwakwalwar mata na da karfin gane maganganun fuska da kaso 70. Sai dai  kwakwalwar nada kashi 10 na gane karyar fatar baki, batare da an kalli juna ba.

Matan sun kware wajen yin karyar ido na ganin ido.

4. Yanayin Magana.

Mata: Kwakwalwar mata na amfani da hanyar lauye-lauye wajen yin magana. Ma’ana basa iya fadar magana kai tsaye ba tare da sun jinginata da wani abun daban ba.

Maza: Kwakwalwar maza na kaisu ga fadin magana kai tsaye bisa abinda zuciyarsu take nufi.

5. Magance motsin Rai/Zuciya

Mata: Sukayi magana mai yawa a lokaci daya ba tare da dogon tunani ba.

Maza: Sunayin tunani sosai kafin furta kalamai.

6. Abinda kowa yafi so.

Maza: Maza suna son girma da daukaka tare da jin dadin warware matsaloli.

Mata: Kyakkyawar dangantaka, ‘yan uwa hadi da son hira.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kashi 18 daga cikin 30 na masu tabin hankali a Najeriya, Mata ne – Likitan Kwakwalwa

Dabo Online

Lemon Tsami yana kare jiki daga daukar cutar “Cancer”, Daga Dr Guru Prasad

Dabo Online

Diclofenac yana kara janyo afkuwar ‘Bugawar Zuciya’ da kaso 50

Dangalan Muhammad Aliyu

Agwaluma na rage karfin maza -Binciken Masana daga Jami’ar Madonna

Muhammad Isma’il Makama

Yayin da take yi wa Maza illa, ‘Agwaluma’ tana yi wa mata maganin cutar cizon Sauro

Dabo Online

Yin Tusa tsakanin Ma’aurata tana ƙara danƙon soyayya – Masana Lafiyar Jiki

Dabo Online
UA-131299779-2