Wasu matasa da adadi yake mai tarin yawa sun yi wa wani tsohon da suke zargi ya yi wa wata yarinya fyade duka bisa abinda suka kira takaitaccen hukunci.
Cikin faifan bidiyon al’amarin da DABO FM ta samu, an hangi mutanen sun umarci tsohon ya kwanta domin ya sha bulala.
Sai dai har yanzu DABO FM ba ta iya gane a ina al’amarin ya faru ba, kazalika ba ta iya gane sunan mutumin ba.
An hangi wanda yake kamar jagoran dukan yana cewa; “Jama’a, masu irin wannan halin fa idan muka kamasu fa ba za tayi musu kyau ba.”
“Duk wani wanda zai kama yara yayi musu fyade idan muka yi karo ba za tayi kyau ba.”
Daga nan ne aka samu wani da igiyar shanya ya rika zabga masa a baya. An jiyo wasu suna cewa ayi masa a Kai.
Birgima, kuka da ihun wayyo tsohon ya yi tayi kafin daga bisani suka kyaleshi.
Sai dai masana suna ganin wannan ba hukunci bane domin yin dukan kadai kamar bayar da kofa ce ga duk mai sha’awar yin fyade idan ya san ba za a mikawa hukuma shi ba.
Kalli bidiyon a nan:
