Home Ra'ayoyiPantami: Wajibi ne wanda ya samu wadata ya ƙi jin dadin rayuwarsa?, daga Hassan

Pantami: Wajibi ne wanda ya samu wadata ya ƙi jin dadin rayuwarsa?, daga Hassan

by Dabo Online
0 comments

Abubuwa da dama da mutane suke kasa fahimta game da halin da Najeriya take ciki shine, akwai wasu mutane da suke samun wata kariya ko wani gata daga bangaren wani abu da ya shafi kundin tsarin mulki, matsayi na kujerar siyasa, alfarma ta sarauta ko ilimin addini musamman fa wadanda suke koyar da karatun addini, wanda Malam Isah Pantami ya kasance daga wannan bangaren.

To sai dai kuma a lokacin da wasu ke kokarin yage ko kawar da waccar alfarma da wadancan mutane suka samu, ta hanyar bayyana wani abu da suka aikata na kuskure ko son zuciya, wani lokacin ma ta hanyar yarfe na siyasa, to daganan ne hankalin wasu magoya baya da masu biyayya(irin ta makancewar nan) za su hayyako ta hanyar mayar da martani da zai iya hadawa da cin zarafin juna da sharri ko aibantawa, wanda hakan ba ya daga cikin koyarwar da shi wanda suke karewa ya yi musu.

A kwanan nan, kafafen yafa labarai sun dau dumi sosai dangane da labarin da sahara reporters ta fara bugawa na cewar Malam Pantami ya sayi wasu mashahuran gidaje guda uku zuwa hudu da ya zuba matansa a ciki. Wanda a cewar jaridar, malami kamarsa bai dace ya yi ta’ammali da irin wadannan gidaje na alfarma ba, musamman a wannan lokaci da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki. To daganan ne fa sauran kafafen yada labarai da sa da zumunta suka dauki dumi, har sauran mutane magoya baya da masu hamayya suke ta musayan kalamai masu siffa da siga launi-launi.

Abin dai nazarin da za a fara dubawa shine, shin Malam Pantami ya sayi gidajen ko kuwa? Kuma a ina ya sayesu? Akan wane kudi? Wanene agent(wakilin cinikin)? Kuma yaushe ya tare ko ya shigar da iyalansa ciki? Daganan ne sai a yi duba na tsanaki a yi masa shari’ah.

Wasu daga cikin masu zafafawa na kalubalantar hakan da cewar, me yasa tun da yake aikin koyarwar a Saudiyya bai sayi gidajen ba sai yanzu? Kuma da yawa sun bayyana Malam Pantami a matsayin wanda ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnati baya tare da mukarrabanta(ciki har da ministoci, irin kujerar da yake Kai yanzu) da cewar ba sa tausayin talakawa da gudanar da rayuwar alfarma da facaka bayan bayin Allah na fafutukar abin da za su yi karin-kumallo.

To koma dai ya abin yake, da yawa daga musulman Afrika ta yamma na kallon malamai a matsayin wadanda bai dace suna rayuwar alfarma da kece rai ni ba. Ya kamata su tsoma zuhudu da tawali’u a cikin gudanawar rayuwarsu. To amma shi Malam Pantami sai ya saba musu ta wannan siga. Wata kila akan hakane suka da kyamar gidajen da ya saya ya zama abin tayar da jijiyar wuya akai.

Daga karshe muke ganin idan har ana so a kara tsaftace wannan zargi, to ya kamata Malam ya futo ya bayyana lokacin da ya fara aikin koyarwa a jami’ar Saudiyya, abin da ya samu na albashinsa, lokacin da ya shiga gwamnatin Buhari ta Najeriya, da kuma duk abin da ya mallaka. Sai masu hankali da tsoron Allah su auna su tankade, su rarrabe aya da tsakuwa akan wannan batu na gidajen alfarma!

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00