Home AzumiYa kamata al’umma su yi amfani da goman karshe wurin komawa ga Allah da naiman gafarar sa-Mustapha Sitti

Ya kamata al’umma su yi amfani da goman karshe wurin komawa ga Allah da naiman gafarar sa-Mustapha Sitti

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

Daraktan agaji na kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatussunnah ta kasa Injiniya Mustapha Imamu Sitti, ya bukaci al’ummar musulmi su yi amfani da wannan lokaci na goman karshe a watan Ramadana wurin tsarkake niyya da komawa ga Allah madaukakin Sarki domin samun sauki a halin da duniya ke ciki game da wannan cutar sarkewar numfashi ta Covid-19, da kuma naiman gafarar sa a kan zunuban da muke aikatawa.

Injiniya Sitti ya bayyana haka ne sa’ilin zantawar sa da Dabo FM a Zariya.

Ya ce, kasancewar azumin bana ya zo da wani salo da al’umma da dama ba su taba riskan irin sa ba, amma ba abun mamaki ba ne kasancewar ko a zamanin baya an samu barkewar annoba.
Kuma kasancewar idan abu ya faru, babban mafita shi ne komawa ga Allah madaukakin Sarki da naiman sauki gare shi saboda babu mai iya yaye wata cuta sai shi.

Ya kara da cewa, a cikin goman karshen na Ramadanan ne, ake samun daren Lailatul Kadari da ya zo cikin Al-qur’ani mai girma cikin Suratul Kadri.

A cewar Imam Sitti bai kamata musulmai su yi Sakaci da wadannan kwanaki su wuce ba tare da sun ribace su ba.

Ya kara da cewa, akwai bukatar sanya al’umma cikin addu’oi musamman wanda suka tsinci kan su a wani hali da ba su saba ba, tare da cigaba da bin umarnin gwamnati da na masana kiwon lafiya domin kare lafiya da dukiyoyi.

Da ya juya ga bangaren gwamnati kuwa, ya naimi ganin ta sassauta akan dokar kulle da ta sanya domin komawa wurin Ibadu da nufin rokon Allah akan wannan yanayi da al’umma ke ciki.
Kasancewar Allah madaukakin Sarki ya ce, Dukkan abun da ya yi tsanani zai yi sauki, kamata ya yi a bar al’umma su koma ga mahalicci su roke shi a kan halin kuncin da a ke ciki.

Da ya juya ga bangaren aikin Gona kuwa, ya ce zuwa yanzu sun ga amfanin manufar gwamnati na kulle iyakokin kasar nan ta kasa domin alkinta abun da ake nomawa a gida, kuma ya bukaci ta cigaba da wadata manoma da takin zamani domin kara inganta amfanin Gona.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00