Labarai

Daukar lauyan da ba Musulmi ba ya jawo wa IZALA cece-kuce

Tin bayan daukar lauyoyin kamfanin Arthur Nylander  da shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau ya yi akan kafar labarai ta Sahara Reporters, al’umma da masu fashin baki suke ta cece-kuce.

A dai cikin makon da muke ciki, Sahara Reporters suka wallafa labarin ‘mutuwar Sheikh Bala Lau’, har ma suka ce an binne shi ba tare da bin tsarin ba da tazara ba kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayar domin kaucewa yaduwar cutar Kwabid-19.

A takardar da kamfanin lauyoyin ya fitar, ya gindaya sharudan da Sahara Reporters zasu cika kafin malamin ya yafe musu, idan suka gaza cikawa kuwa, zasu biya diyyar zunzurutun kudi na Naira miliyan 100.

Babban abin da masu cece-kuce suke magana akai shine yadda lauyoyin suka kira kungiyar IZALA  da sunan “Kungiyar masu Bidi’a” a maimakon Kungiyar masu kawar da Bidi’a. Har ma suke cewa; “duk musulmin an rasa manyan lauyoyi da zasu wakilci shugaban kungiyar Musulunci?

Ga dai yadda wasu daga cikin masu bayyana ra’aoyinsu a kafafen sadarwa suka bayyana:

Sai dai tin ranar, Sahara Reporters ta janye labarin da ya rawaita na ‘mutuwar’ Sheikh Bala Lau har ma tayi sabo inda tace yana raye, ta kuma wallafa bidiyon da shehin malamin yayi maganar cewa yana nan a raye. Hakan yasa wasu ke ganin maganar lauyoyin ba ta da wani tasiri domin abinda suka bukata, jaridar ta riga tayi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kungiyar Izala tayi kiran Sanatoci da kada su tantance Ministocin da suke ‘yan Shi’a

Dabo Online

Kungiyar Izala ta kai ziyarar jaje ga Sambo Dasuki kwanaki 3 bayan sakinshi akan zargin “Sata”

Dabo Online

Kudin Makamai: Abinda kayi mana, baza mu manta ba – IZALA ta fada wa Sambo Dasuki

Dabo Online

A tantance jami’an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

Muhammad Isma’il Makama

Sheikh Bala Lau ya ziyarci filin masallacin da aka rusa a Fatakwal dake Jahar Ribas

Muhammad Isma’il Makama

Tarihi: Sarkin Musulmai Sir Abukabar III ne ya rada wa kungiyar IZALA suna

Dabo Online
UA-131299779-2