Home LabaraiKwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

Kwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

by Dabo Online
0 comments
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudurinta na yi wa dukkanin almajiran da suke jihar Kano gwajin cutar Kwabid19 dake jihar Kano.

Gwamna Dr Abdullahi Ganduje ya ce gwamnatin jihar za tayi haka ne domin bai wa almajiran da suke jihar kariya ta musamman bisa hadarin da almajiran suke tunkara kasancewa sun kasance suna zama wajen cunkuso a ko da yaushe.

Tini dai gwamnan ya fara shirin kafa kwamitin gaggawa da zai yi duba akan hanyoyi taimaka musu tare da basu kariya a cikin yanayin da ake ciki na cutar Kwabid19 da ta addabi duniya baki daya, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gwamnan yace; “Mun yanke shawarar gwada dukkan almajiran jihar Kano da niyyar  basu kariya. Duk wadanda basu dauke da cutar za mu mayar da su jihohinsu, wadanda suke da cutar za a basu magani tare da shaidar NCDC idan sun warke.

[penci_related_posts dis_pview=”no” dis_pdate=”no” title=”Masu alaka” background=”” border=”” thumbright=”no” number=”2″ style=”list” align=”none” withids=”” displayby=”tag” orderby=”rand”]

“Mun shirya Iliminatar da almajiran Kano. Wadanda ba su da wurin zuwa, mune iyayensu kuma zamu kula da su. Yaranmu na da hakkin samun ilimi, zamu tabbata mun hade karatun da na Boko. Domin duk su na hakkin da zamu ilimantar da su.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00