(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Yanzu an inganta tashar KSMC Queen FM da kayayyakin watsa shirye-shirye na zamani-Tanimu Albarka

Karatun minti 1

Anyi kira ga masu sauraran kafar yada labarai na rediyon jihar Kaduna ksmc Queen fm Zaria, da su rinka tallata hajojin ko sanarwarar tarurruka don cigaban tashar.

Yace, yanzu haka gwamnatin Jihar Kaduna ta fara inganta tashan da kayayyakin aiki na zamani donmin cigaban tashan.

Shugaban ƙaramar tashar radiyo jihar Kaduna da ke Zariya Ksmc Queen FM Malam Tanimu Albarka ya fadi haka ne a lokacin da aka gudanar da zaben shuwagabannin kungiyar masu sauraran Shirin Wasa kwakwalwa da ake gabatarwa a tashan, duba da yadda Shirin ya sami karbuwa ga Jama’a.

Shugaban karamar tashan dake Zaria, Mal. Tanimu Ibrahim Albarka, da babban injini na tashan Alh. Haruna Sidi Bamalli ya wakiltan.

Mai gabatar da shirin, Mal. Musa Dogara, ya godewa daukacin masu sauraron Shirin da bada tallafi don inganta shi, inda ya shawarce su da su hada kan su don cigaban kungiyar da tashan ta Queen fm Zaria.

Sabon shugaban kungiyar, Mal. Tanimu Shehu, yayi kira da membobin kungiyar da su bashi hadin kai don ciyar da kungiyar gaba, yayi alkawarin jagoranci bisa gaskiya da rukon amana.

An zabi Tanimu Shehu a matsayin shugaba, Hajiya wusasa maman Dalladi magume a matsayin shugaban mata, Aminu sirrin bege Jami’in hudda da Jama’a da sauran su.

Taron ya sami halartan Shugaban sashin shirye-shirye ta tashar Queen fm Mal. Salihu Adamu, Injiniya Haruna sidi makarfi, zakiru mika’ilu dogarawa da sauran masu sauraro.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog