Jami’ar Ahmadu Bello ta sanar da ranar komawa karatu : 25 ga Janairu

Karatun minti 1

Jami’ar Ahmadu Bello ta sanar da ranar 25 ga Janairu a matsayin ranar da za a cigaba da karatu a makarantar.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Auwalu Umar ya fitar, ta ce hukumar gudanarwar jami’ar ta fitar amince da komawarar a yayin zaman da tayi a yau Talata.

Sai dai sanarwar ta ce za a koma makarantar ne bisa tsarin rukuni-rukuni.

Rukunin farko da za a fara komawa sun hada da daliban ajujuwan karshe da dukkanin bangarorin karatun jami’ar, dukkannin daliban lafiya, daliban aji daya da ‘yan aji 2.

Kazalika ta ce daliban da suka yin digiri na 2 za su cigaba da daukar darasi a yanar gizo gizo.

Rukuni na biyu ya tsarin komawar, wadanda su ne za su koma daga baya sun hada da; kafatanin daliban aji 3 na dukkanin bangarorin makarantar, daliban aji 4 da kuma 5, da duk sauran dalibai.

Sai dai sanarwar ta ce jami’ar a shirye take ta sauya daga matsayar komawar karatun idan har ta samu umarni daga gwamnatin tarayyar Najeriya ko ta jihar Kaduna.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog