An inganta tashar KSMC Queen FM da kayayyakin watsa shirye-shirye na zamani -Tanimu Albarka

Karatun minti 1

An yi kira ga masu sauraren gidan rediyon KSMC QUEEN FM da ke  Zaria a jihar Kaduna, da su rika tallata hajoji ko  bayar da sanarwarar tarurruka don cigaban tashar.

Shugaban karamar tashar rediyon, Mallam Tanimu albarka ne yayi wannan kira dai dai lokacin da aka yi zaben shugabannin masu sauraren shirin Wasa Kwakwalwa da ake gabatarwa a gidan Rediyon.

Shugaban ya ce yanzu haka gwamnatin Jihar Kaduna ta fara inganta tashar da kayayyakin aiki na zamani domin cigaban tashar.

Shugaban ya samu wakilcin babban Injiniyan tasahar, Alhaji Haruna Sidi Bamalli a yayin da aka gudanar da zaben a ranar Litinin din da ta gabata.

Mai gabatar da shirin Wasa Kwakwalwa na rediyon, Mal. Musa Dogara, ya gode wa daukacin masu sauraron shirin da wadanda suke bada tallafi don inganta shirin, inda ya shawarce su da su hada kan su don cigaban kungiyar da tashar ta Queen FM Zaria.

Sabon shugaban kungiyar masu sauraron shirin, Mal. Tanimu Shehu, ya yi kira ga membobin kungiyar da su bashi hadin kai don ciyar da kungiyar gaba, ya yi alkawarin jagoranci bisa gaskiya da rikon amana.

An zabi Tanimu Shehu a matsayin shugaba, Hajiya Wusasa maman Dalladi Magume a matsayin shugabar mata, Aminu Sirrin Bege Jami’in hulda da Jama’a da sauran su.

Taron ya samu halartar shugaban sashin shirye-shirye na tashar Queen FM, Mal. Salihu Adamu, Injiniya Haruna Sidi Makarfi, Zakiru Mika’ilu Dogarawa da sauran masu sauraro.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog