Allah Ya yi wa Alhaji Muhammadu Dauda Dangalan, daya daga cikin iyayen jami’iyyar NEPU rasuwa.
Babban ‘dan mamacin, Alhaji Ali Baba Muhammad ne ya shaida wa DABO FM.
Ya rasu yau Asabar bayan fama da rashin lafiya a gidansa da ke unguwar Fagge a jihar Kano.
Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 5 na yamma a gidansa da ke Fagge.