Dangalan: Tabbas mun yi rashin shugaba abin koyi -Ganduje

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya bayyana rasuwar Dattijo Dauda Dangalan a matsayin babban rashi a Kano da Najeriya.

A cikin sakon ta’aziyyar da gwamnan ya aike wa iyalan marigayin, ya ce labarin mutuwar Dangalan, ya firgita shi sosai,

Gwamnan ya kara da cewar tabbas mutuwar Dangalan tamkar faduwar durakun dimokradiyya ne kuma rashi ga talakawan Najeriya domin ya yi rayuwarsa ne wajen nema wa talaka ‘yanci.

“A madadin gwamnati da daukacin al’ummar jihar Kano, ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalan Malam Dauda Dangalan da dukkanin talakawan Najeriya.”

Gwamnan ya kuma roki Allah da ya gafarta masa Ya kuma albarkaci zuriyarsa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog