(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Yanzu Yanzu: Gwamnati ta fara hukunta masu hannu a kisan Mr Johnson Kolade

Karatun minti 1

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta fara hukunta jami’anta da ke da hannu wajen harbe Mr Johnson Kolade.

Tini dai rundunar ta dakatar da Insfecta Ogunyemi Olalekan, jami’in SARS daya harbe Mr Kolade a ranar Lahadin data gabata.

An kuma mika shi zuwa shashin binciken masu aikata manyan laifuka domin cikakken bincike tare da tisa keyarshi zuwa kotu.

Mai magana da yawun rundunar na jihar Legas, Bala Elkana yace rundunar ta yanke hukuncin ne bayan shafe kwanaki 4 suna bincike tin bayan kisan.

[the_ad id=”5121″]

 

Shafin Sahara Reporters ya rawaito cewa ‘Yan sanda biyu (CSP Indyar Apev da Ofunyemi Olalekan) aka kama da bisa laifin harbe Mr Johnson ba bisa ka’ida ba, inda hukumar ta dakatar dasu tare da mika su wajen binciken kwakwaf.

Tini dai rundunar ta aikewa CSP Indyar takardar sallama tare da garkameshi zuwa shashin binciken CID.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog