(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Shugaba Buhari ya dauki hanyar zuwa kasar Jordan da Dubai

Karatun minti 1

Yau Alhamis da misalin karfe hudu da ‘yan dige-dige, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki hanyar zuwa kasar Jordan.

Shugaban zai halarci taro a babban birnin kasar na Amman tare da wasu shugabanni kasashen duniya.

Taron zai maida hankali ne akan tattauna batutuwan tattalin arziki na duniya musamman a nahiyar arewacin Afrika dama daular larabawa.

Ana saran gudanar da taron a yau Alhamis.

Bayo
Lokacin da shugaba Buhari yake sallamar tafiya

Daga bisani zai bar birnin Amman a ranar Lahadi zuwa Dubai, inda zai shiga wani taron zuba jari na shekara-shekara bisa gayyatar Sarki Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar Gwamnan jihar Jigawa, Malam Abubakar Badaru, da takwaranshi na jihar Oyo, Ajimobi da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.

Akwai mukarrabai irinsu Ministan harkokin kasashen waje na fadar gwamnatin Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari yanata cigaba da shan suka bisa yin shiru da rashin daukar mataki akan kisan gillar da akeyi a jihar Zamfara.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog