Kano: An shigar da kararraki 33 akan zaben Kano

Kotun zabe a jihar Kano ta kaddamar da fara zaman sauraron kara a yau Alhamis, 04/04/2019.

Alkalan da zasu jagoranci kararrakin sun hada da Mai shari’a Nayai Aganaba a matsayin shugaban kwamatin sauraron karar, inda Mai Shari’a Ashu Augustine Ewah da Mustapha Tijjani a matsayin membobin kwamitin.

Shugaban alkalan ya bada tabbacin yin adalci tare da yin shari’a bisa doka da kuma kaucewa kutse ga wani bakon haure.

TALLA

An shigar da kararraki 33 gaban kotun a jiya Alhamis da kotun da fara zama.

An samu kara bisa zaben ‘yan majalissun tarayya dana jiha.

Karar Majalissar Jiha guda 22 inda aka shigar da ta majalissar tarayya 11.

Masu Alaƙa  Sakamakon zabe kai tsaye daga birnin Kano da kewaye

 

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.

%d bloggers like this: