(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zaftarar albashi: ‘Alaƙar Gwamnatin Kano da yankan aljihu’

Karatun minti 1
Gwamna Abdullahi Ganduje (Kano) - APC

Tin bayan da gwamantin jihar Kano ta fara zaftare wa ma’aikatan jihar musamman yan fansho albashinsu, fitattu mutane musamman malamai suka rika bayyana ra’ayoyinsu dangane da abin da suka kira ‘aika-aika da rashin tausayi.’

Abin ya kai har fitattun malamai sun fara tsokaci a kan lamarin. Babban malami, Farfesa Umar Muhammad Labdo, malami a jami’ar Yusuf Maitama Sule ta jihar Kano, ya alakanta Gwamnatn jihar Kano da ‘Gwamnatin ‘yan sane masu yi wa ma’aikata da  yan fansho yankan aljihu.’

Malamin ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Juma’a.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya, kungiyar ‘yan jaridu ta yi kira ga gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da ya biya kudaden da ya yanke wa yan fansho da wasu ma’aikata a jihar Kano.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog