Ƴan Najeriya su shirya wa ƙarin kuɗin haraji zuwa 10% cikin kasafin kuɗin 2021 -FG

Karatun minti 1

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na ƙara kudin haraji da kashi 2.5% cikin shekarar 2021 a wani yunƙuri na ƙara samun kuɗaɗan shiga.

Dabo FM ta rawaito Ministar Kudi, Dr Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a ranar Talata lokacin da take bayyana yadda kasafin kudin shekarar 2021 zai kasance a gaban kwamitin kudi na majalisa wanda Hon. James Faleke yake shugabanta.

Idan ba a manta ba a farkon shekarar nan, 1 ga Fabarairu gwamnatin ta yi karin haraji zuwa kaso 7.5% wanda ya jawo cece-kuce, idan har sabon ƙarin ya tabbata kuɗin haraji zai kai kaso 10% kenan wanda ka iya jawo karin hauhawar farashi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog