An binne dan Najeriya da ya rasu a kasar Indiya bisa koyarwar addinin Musulunci

by Dabo Online
0 comments

Tini dai aka kammala binne dalibin nan , dan Najeriya da ya rasu bayan kammala karatun Digirinshi na 2 a kasar Indiya.

DABO FM ta tabbatar da binne Sulaiman a daren ranar Alhamis 18 ga watan Yulin 2019.

A0B7A28E C422 42DF B91D 88C928F88460 - Dabo FM

Wakilin DABO FM dake kasar Indiya ya tabbatar da binne Suleiman da misalin karfe 9:17 na dare a lokacin kasar Indiya, wanda yayi dai dai da 4:48 na yamma agogon Najeriya da Nijar.

1DE7CD82 23B5 427C AED1 9F4131562ED5 - Dabo FM

An dai binne shi ne a unguwar Amer dake garin Jaipur na jihar Rajasthan, arewacin kasar Indiya.

B4EF6E07 6AF6 485D ABB9 E2741A5E6EF5 - Dabo FM

Sulaiman, mai shekaru 26, dan asalin jihar Adamawa, ya rasu a ranar Laraba biyo bayan matsananciyar cuta.

Hakan yana zuwa ne a dai dai lokacin da yake jiran karbar takardar shaidar kammala karatun Digirinshi na 2 a jami’ar NIMS University dake kasar Indiya.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00