Labarai

Al-Zakzaki ya nemi kotu ta bashi izinin zuwa kasar Indiya domin duba lafiyarshi

Shugaban Kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky tare da matarshi, hadi da ‘yarshi Zinat, sun rubutawa babbar kotu a Kaduna, bukatarsu ta tafiya kasar Indiya domin duba lafiyarsu.

Yanzu haka dai shugaban kungiyar,Sheikh Zakzaky yana hannun jami’ai bisa tuhumar laifuffuka da suka hada da taron mutane ba bisa ka’ida ba, kisan kai tare da takurawa mutane hadi da wasu laifuffukan.

Da yake magana da manema labarai, Dari Bayero, Daraktan hukunce-hukunce da suka shafi mutane, ya bayyana cewa kotu zata zauna akan batu ranar Alhamis.

Bayero yace shugaban kungiyar, Zakzaky, ya turo da neman izini na bukatar zuwa asibitin Metanta dake New Delhi, babban birnin kasar Indiya, tare da dawowa Najeriya don cigaba da shari’ar shi da akeyi da zarar asibitin ya sallameshi.

Bayero yace a ranar 18 ga watan Yuli, mai shari’a D.H Khobo zai zauna don yin duba akan bukatar da shugaban kungiyar ya aike wa kotun.

Idan ba’a manta ba dai mai shari’a Gideon Kurada, wanda karar take a hannunshi, ranar 25 ga watan Afirilu ya dake zaman shari’ar har illa mashaa Allahu.

Dage zaman na zuwa ne domin baiwa mai shari’ar damar zama alkalin kotun karbar korafe korafen zaben shekarar 2019.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kungiyar IMN ta Shi’a tace ta dakatar da Zanga-zangar da ta shekara 4 tana yi akan sakin Zakzaky

Dabo Online

Shugaban tsohuwar kungiyar IMN ta Shi’a, Mal. Ibrahimul Zakzaky zai tafi kasar Indiya a yau

Dabo Online

‘Yan Shi’a sun kashe DCP Umar Usman tare da cinnawa motocin ‘NEMA’ wuta

Dabo Online

Kotu ta ayyana Kungiyar Shi’a a matsayin Kungiyar Ta’addanci tare da haramta ta a Najeriya

Dabo Online

‘Yan Sanda su bude wuta akan Yan Shi’a dake zanga-zanga a Abuja

Dabo Online

Yanzu-yanzu: An Gwabza da ‘Yan Shi’a da Jami’an Tsaro

Rilwanu A. Shehu
UA-131299779-2