Ganduje ya kaddamar da kwamitin don fara shirin Ruga a Kano.

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya kaddamar da kwamitin da zai yi duba akan tsare tsare da tunkara shirin yin Ruga don makiyaya a jihar Kano.

Ganduje ya kaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis a fadar gwamntin jihar dake birnin Kano.

DABO FM ta rawaito daga DAILY NIGERIAN cewa; Dr Jibrila Ahmad ne zai shugabanci kwamitin.

Ganduje ya baiwa kwamitin makwannin 3 domin hada bayanai.

Da yake magana da manema labarai bayan kaddamar da kwamitin, Ganduje yace shirin gina Ruga a jihar Kano, zai kawo karshen gararamba da makiyaya suke yi.

Ya kara da cewa shirin zai kara bunkasa tallalin arziki tare da kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake alkanta Makiyaya da samarwa.

%d bloggers like this: