Diyar shugaba Muhammadu Buhari, Zahra Muhammad Buhari, ta shirya taro domin tattaunawa da mutane akan batutuwan yanar gizo.
DABO FM ta tattara cewa Zahra Buhari, zata yi magana da mutane mai taken ‘Maraice da Zahra’ tare da basu shawarwari akan yacce zasu kauracewa barazanar da akeyi musu a yanar gizo-gizo.
Zahra, ta sanya Naira 10,000 a matsayin kudin yin rijista domin shiga wajen taron.
Za a gudanar da taron a ranar 10 ga watan December, kamar yacce ta bayyana a shafinta na Instagram.