Goyan bayan sana’ar ‘Ya tin da farko a mai makon ayi mata tanadin shagalin bikin ta, ana kashe kudi da al-mubazzaranci da dukiya duk da sunan farin cikin aure wanda hakan bashida wata ma’ana a addini, a kan a iya cewa ma wata hanya ce ta saka karya a cikin rayuwa.
Da yawa hakan yana hana wasu mazan aure saboda wasu dangin bazasu baka ba aure ba idan har baka kama wajen bikin da sukeso ba saboda wannan sai a daga bikin koma a fasa auren da kai wanda hakan babbar matsala ne.
Aure dai anayi ne saboda sunnar annabi (SAW) ce da kuma kauracewa shiga halaka amma a wasu bangarorin ana mayar dashi wani abu daban wanda da yawa auren baya dadewa.
Ina ganin da kashe wadannan kudin gwanda a hada a kai ta makarantar koyan sana’o’i domin ta samu horo akan sana’ar da take da buri, a bata jari ta tafi gidan mijinta yafi a kashe kudin a yini guda ko biyu a banza, idan kuma karatu take a taimaka mata tasamu ta gama a sama mata hanyar dogara da kanta yafi duk shagulgulan bikin da za’a shirya mata.
Edreez Abdulaziz Sani
