Wani Likita a kudancin kasar Indiya, ya samu nasarar ciro Kifi a cikin hancin wani Yaro a kasar Indiya.
DABO FM ta tattaro cewa; Yaron ya gamu da iftila’in shigewar Kifin cikin hancinshi bayan ya fada cikin wata tamkekiyar Rijiya dake kusa dasu gidansu a jihar Tamil Nadu.
DABO FM ta tattara cewa; yayin fadawar Yaro cikin Ruwan da ya kusa nutsar da shi, anan Kifin ya samu nasarar shigewa cikin Hancin nashi.
Likita, Kathiravan, ya bayyana yacce aka kawo Yaron mai suna Arul Kumar, cikin rashin nutsuwa tare da rashin yin kyakkyawan numfashi, lamarin da yace yasa suka fara bincike domin taimakon Arul Kumar.
Ya bayyana yacce aka shafe tsawon mintuna 30 kafin a iya zakulo Kifin daga cikin hancin Yaron.
