Home Kiwon LafiyaKo kunsan laifi ne siyar da tabar sigari ɗai-ɗai a Najeriya saboda gurbacewar yara?

Ko kunsan laifi ne siyar da tabar sigari ɗai-ɗai a Najeriya saboda gurbacewar yara?

by Dabo Online
0 comments

Gwamnatin Najeriya ta haramta siyar da tabar sigari a dai-dai a dukkanin inda aka sahale a siyar da taba.

Gwamnatin tayi dokar ne bisa arhar da tabar tayi wanda dalilin haka ne ya sanya yara suke siyar tabar suna sha.

DABO FM ta binciko cikin dokar taba da gwamnatin Najeriya ta sabunta a 2015 wato Nigeria Tobacco Control Act 2015, inda ta haramtawa masu dillancin sigari siyar da ita dai-dai, sai dai a siyar da kwali.

Haka zalika dokar ta haramtawa masu dillancin taba siyarwa da wandanda basu kai shekara 18 ba.

Dokar tace dole ne masu siyar da taba su tabbatar da shekarun wanda zasu siyarwa ta hanyar ganin katin shaida (ID Card) na gwamnati.

Dokar dai tace duk wanda aka kama da aikata wannan haramtaccen aikin, za’a ci shi tarar N200,000 ko kuma daurin shekara daya a gidan gyaran hali.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00