Attajirar Najeriya ta bawa Najeriya tallafin Naira biliyan 1, zata rabawa Zaurawa da Marayu N25,000

by Dabo Online
0 comments

Folorunsho Alakija, attajirar da babu kamarta a Najeriya zata rabawa Zawarawa da marayu masu rijista a Najeriya N25,000 kowannensu.

Hakan na zuwa ne kwana 1 kacal bayan da ta bawa gwamnatin Najeriya tallafin kudin yakar Coronavirus kimanin Naira biliyan 1.

DABO FM ta tattara cewar Miss Florunsho Alakija zata baiwa marayu da zaurawa kudin ne a karkashin gidauniyarta mai taken ‘The Rose of Sharon’

A wata sanarwa da attajirar ta fitar a shafinta na twitter ranar 30 ga watan Maris, tace attajirar tare da mijinta Mista Modupe Alakija a karkashun kamfaninsu na Famfa Oil sun alkauranta baiwa Najeriya tallafin biliyan 1 domin yaki da Coronavirus.

Haka zalika a yau 31 ga watan Maris, attajirar tace zata raba kudaden ne ga dukkanin Zaurawa da marayu a Najeriya da suke da rijista a fadin jihohin Najeriya 36 da tarayya Abuja.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00