Tun bayan dokar hana walwala na tsawon awa 24 da gwamnatin Jihar Kaduna ta kakaba tun a ranar Alhamis 24 ga watan Maris din nan. Yanzu haka al’ummomi da dama sun amsa kira tare da dukufa wurin taimakwa marasa karfi da suke cikin halin kunci na cin yau da kullum.
Daya daga cikin irin wadannnan al’ummomin, shi ne tsohon dan takarar majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Zariya kewaye Hon Alhaji Ibrahim Garba Umar Madalla.
Rabon kayan abincin da suka hada da Shinkafa da Taliya da kuma sauran abubuwan more rayuwa, mutane da dama ne suka amfana a yankin karamar hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.
Da yake zantawa da Dabo FM jim kadan bayan rabon kayayyakin, Hon Ibrahim Madalla, ya ce, ya zama wajibi al’umma su koma ga Allah a halin da Najeriya da ma sauran kasashen duniya suka tsinci kansu a yau, saboda cutar da ta kunno wanda yanzu haka ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 2 baya ga mutane sama da 100 da suka kamu a kasar nan kadai.
Ya nuna takaicin sa kan yadda wasu ke bijirewa shawarar masana kiwon lafiya da umarnin da gwamnati ta bayar na takaita zirga-zirga da shirya taruka, inda ya kwatanta hakan a matsayin bijirewa umarnin Allah da ya tilasta yima shugaba da’a matukar bai saba ma umarnin Allah ba.
Hon Ibrahim Garba, ya ce ba yanzu ne kadai cuta ke ratsa dukkanin duniya ba, ko lokacin annabawan Allah da sahabban sa an samu jarabawa na wasu cututtuka a wancan lokacin.
Ya roki yan kasuwa su yiwa Allah su guji tsawwala kudi a kayayyakin masarufi da na lamuran yau da kullum.
Sannan daga karshe ya hori al’umma su dauki dabi’ar wanke hannu da zaman gida da kuma daina shiga Jama’a barkatai kamar yadda gwamnati da masana kiwon lafiya suka bada shawar-wari.
