Home LabaraiMudassir & Brothers ya rarraba tulin buhuhunan shinkafa a Kano

Mudassir & Brothers ya rarraba tulin buhuhunan shinkafa a Kano

by Dabo Online
0 comments

Kamfanin Mudasssir & Brothers dake da shedikwata a jihar Kano, ya rarraba buhuhhunan shinkafa masu tarin yawa a jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewar kamfanin ya rarraba shinkafa karamin buhu mai nauyin kilo 25 a unguwar Yalwa dake karamar hukumar Dala a birnin Kano kamar yadda wakilinmu ya ganewa idanuwansa a yau Alhamis.

DABO FM ta shaidawa idanuwanta yadda motar kamfanin na Mudassir & Brothers ta rika bi gida-gida tana rabawa mabukata da rana zuwa yammacin yau Alhamis tin daga karfe 1 na rana. Kafin daga bisani motar ta tsaya ana zuwa a karba, kamar yadda zaku gani a bidiyon kasa.

A zantawar wakilinmu da wanda ya jagoranci rabon shinkafar wanda ya bukaci mu sakaye sunanshi, ya bayyana cewar shugaban kamfanin, Alhaji Mudassir Idris Abubkar ne ya umarcesu da su rabawa mutane shinkafar.

“Alhaji Mudassir Idris Abubakar, shi ne ya bamu umarnin mu rabar da shinkafar nan, yace mu rabawa mutane har sai ta kare.”

“Tin jiya muke rabo, gashi yau munayi, gobe ma zamuyi har sai ta kare. A iya yau ma mun rabar da kusan buhu 1000.”

A nasu banagren, wadanda suka amfana da rabon shinkafar sun bayyana matukar jin dadinsu bisa ga tagomashin da suka samu.

Wani da muka zanta dashi, Auwal Abdulkadir Yahaya, ya bayyana jin dadinshi bisa ga shinkafar da ya samu tare da nuna godiyarshi ga kamfanin bisa abinda ya kira da aikin alheri.

Haka zalika yayi kira ga masu hannu da shuni da suyi koyi da irin aikin shugaban amfanin na Mudassir & Brothers, Alhaji Mudassir Abubakar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00