Home Kiwon LafiyaHaramun ne siyar da karan ‘Taba Sigari’ guda daya a Najeriya, sai dai kwali

Haramun ne siyar da karan ‘Taba Sigari’ guda daya a Najeriya, sai dai kwali

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Gwamnatin Najeriya ta haramta siyar da tabar sigari a dai-dai a dukkanin inda aka sahale a siyar da taba, sai dai a siyar da kwalin gaba daya.

Gwamnatin tayi dokar ne bisa arhar da tabar tayi wanda dalilin haka ne ya sanya yara masu kananan shekaru su ke siya tabar suna sha.

Haramcin na kunshe a cikin dokar Nigeria Tobacco Control Act da aka sabunta a 2015, kamar yadda DABO FM ta binciko.

Dokar ta ce an haramtawa masu siyar da taba sigari siyar da ita gudanta daya wadda bata wuce N10 zuwa N20 ba a yunkurin gwamnati ta hana yara ‘yan kasa da shekara 18 samun damar siyan tabar.

Kazalika dokar ta haramtawa masu dillancin taba sigari siyar wa da wandanda basu kai shekara 18 ba.

Dokar tace dole ne masu siyar da taba su tabbatar da shekarun wanda zasu siyarwa ta hanyar ganin katin shaida (ID Card) na gwamnati.

Dokar dai tace duk wanda aka kama da aikata wannan haramtaccen aikin, za’a ci shi tarar N200,000 ko kuma daurin shekara daya a gidan gyaran hali.

 

 

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00