A gaggauce: ‘Bam’ ya tashi a Katsina

by Dabo Online
0 comments

An samu fashewar wani abu da ake tunanin Bam ‘IED Bomb’ ne  a kauyen Yammama dake karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Rahotanni sun ce abin fashewar ya tashi ne da safiyar Asabar a gonar wani mutum mai suna Alhaji Hussaini Mai Kwai, DABO FM ta tabbatar.

Kazalika Daily Trust ta rawaito cewar wasu shaidun gani da ido sun ce a kalla mutane 6 ne suka rasu sakamakon fashewar abubuwan.

“Na kirga gawarwaki 6 in da aka garzaya da wasu 5 zuwa asibiti. Jami’an tsaro suna kewaye da wajen a yanzu haka.”

Sai dai har zuwa yanzu, jami’an tsaro basu fitar da adadin wadanda suka rasu a sakamakon fashewar abubuwan ba.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da faruwar al’amarin ta hannun mai magana da yawunta SP Gambo Isah.

Karin Labarai

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00