Kano: Bayan lashe biliyan 4.5, Gadar Dangi za ta kara lashe miliyan 724 ta fidda magudanar ruwa

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kano ta zartar da karin kashe naira miliyan 724,181,938.65 a gagarumin ginin gadar sama data kasa wadda take aiwatarwa a shatale-talen Dangi.

DABO FM ta tattara cewa kamfanin Triacta Construction ne ya samu kwangilar ginin katafariyar gadar a Afrilun 2018 akan kudi naira miliyan dubu 4.5 daka wajen gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Tunda fari an shirya aikin ne domin rage cunkoson daya addabi titin Zaria, Zoo Road da Silver Jubilee, aikin dake cikin wata na 27, kafin fara aikin ansa ran za’a karkare cikin watanni 10 ne.

Daya kaddamar da aikin, gwamna Ganduje ya bayyana cewa “Wannan gagarumin aiki zai ci naira biliyan 4.5, domin ganin anyi aikin ba tare da wata matsala ba mun bawa kamfanin da zai aikin rabin kudin sa, kamar yadda ya bayyana mana nan zuwa watanni 10 an kammala aikin.”

Da yake sanarwa manema labarai bayan kammala zaman sati-sati na majalisar zartarwa, Muhammad Garba ya bayyana gwamnatin ta kara wannan kudaden ne domin karin aiki akan gagarumar gadar.

Cikin aikin da aka kara akwai fidda magudanen ruwan da zasu kai har Geza/Tukuntawa, kana da fidda hanyoyi, tare da gyara titunan Ibrahim Dabo da Bala Borodo. Kamar yadda DailyFocus ta fitar.

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog