0
Kungiyar ta Liverpool ta samu nasara a wasan ta na ranar asabar da ta kara da takwararta ta Brighton & Hove Albion.
Liverpool din dai ta shiga matsi tin bayan shigar sabuwar shekara inda ta kasa cin wasannin da ta buga a farkon shekarar.
Gwarzon dan wasan Afrika, Mohammed Salah ne ya samu nasarar jefa kwallon da ta baiwa kungiyar ta Liverpool damar bada tazarar maki 7 a kan tebur.
Kungiyar da Jorgen Klupp ke jagoranta dai itace ja gaba a teburun gasar firimiyar kasar Ingila da maki 57.
