Mutumin mai suna Victor Odungide ya yi wannan furuci a shafinshi na Twitter @vikolo2000
Hakan ya biyo baya ne bayan shugaba Buhari ya wallafa wani sako a shafinshi na Twitter, inda yake bayyanawa al’ummar Najeriya cewa bazai raba kudi daga asusun kasar ba domin yakin neman zabe.
” Wawa kawai! Wallahi sai na kashe ka da kaina in har kayi nasara. Kaine sular rasa aiki na tin shekarar 2017 hakan yasa bana iya biyan kudin makarantar ‘da na. -Victor
Hukumar manhajar twitter dai ta dakatar da Odungide daga amfani da manhajar ta.
Daga daya bangare kuma mutane, masu amfani da manhajar sunyi ta sanar da hukumomin tsaro domin daukar mataki na gaggawa.
Victor Odungide dai yayi furucin sau uku kamar yadda kuka gani a hotuna.