/

Ighalo zai maye gurbin Suarez a Barcelona

Karatun minti 1

Dan wasan gaban na Super Eagles Edion Ighalo yana cikin ‘yan wasan da Barcelona ke nema domin maye gurbin Munir El Hadadi da Denis Suarez.

Jaridar Sifaniya ta rawaito cewa dan wasan gaban na Super Eagles, Edion Ighalo na gaba gaba cikin sahun ‘yan wasan da kungiyar ta Barcelona ke zawarci.

Wata jaridar sirri ta bankado wani bayani da ya nuna kungiyar tana son samun dan wasa mai arha.

Edion Ighalo ya katse kwantiraginshi daga kungiyar Changchun Yatai dake kasar China bayan da suka koma buga rukuni na biyu a gasar ta kasar China.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog