Home LabaraiAmarya ta gamu da Ajalinta a Hanyar gidan Miji

Amarya ta gamu da Ajalinta a Hanyar gidan Miji

by Rilwanu A. Shehu
0 comments

A ranar Lahadin data gabata ne wata amarya da aka daura aurenta a garin Gashu’an jihar Yobe, ta gamu da ajalinta a garin Buji ta karamar Hukumar Buji a jihar Jigawa, a kan hanyar su ta tafiya gidan miji Jos babban birnin jihar Plateau.

Hatsarin dai ya afku ne a kan kwanar barin garin Buji, wacce take takurarra direbobi ba sa sanin yanayin kwanar in baki ne.

Amarya ta gamu da ajalinta ne tare da kwawayenta guda 5 dake cikin mota kirar sharoon bayan wannan hatsari.

Ganau ya tabbatar wa da wakilin mu na jihar Jigawa faruwar al’amarin.

Ba su rasuwar mutane shida, an garzaya da wasu zuwa Asibiti cikin mawuyacin hali.

Tuni jami’an tsaro suka dauki gawawwakin don mika su ga iyayen su dake garin Gashu’an jihar Yobe.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00