Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya karrama wata malamar firamare, Mrs Obiageri Mazi wadda ke riga kowa zuwa makaranta da wuri kyautar makudan kudade.
Majiyar Dabo FM ta bayyana gwamnan cikin wani fai fan bidiyo daya wallafa yayin wata ziyarar bazata da ya kai makaran tar Shehu Sanda Kyarimi 2 Primary School domin duba gyare gyaren da za’a yiwa wannan makaranta.
Cikin mamaki, gwamna Zulum ya bayyana cewa “Da duku-duku misalin 6:30 na safe na kai ziyara wata makarantar firamare, na hadu da daya daga cikin malaman makarantar Malama Mazi, yan asalin jihar Abia kuma yar kabilar Ibo tazo makaranta tana jiran daliban ta.”
“Kimanin shekaru 31 tayi tana koyarwa. A matsayina na gwamna ina alfahari da ita.”
Matar ta fadi kasa cikin hawayen farin ciki tana godiya tare da addu’a ga gwamnan.
