Labarai

Fiye da talakawa miliyan 5.4 ke karbar N5000 a kowanne wata a Najeriya -Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kimanin talakawan Najeriya miliyan 5.4 ke karbar tallafin naora dubu biyar a kowanne wata.

Majiyar Dabo FM ta bayyana hakan ne bayan wani bayani na hukumar ‘National Social Safety Nets Coordinating Of Nigeria ‘ ((NASSCO), dake bayyana gwamnatin tarayya ta fidda talakawan kasar 5,433,394 daga talauci wanda kowannensu ke karbar naira 5000 duk wata.

Hukumar NASSCO ta bayyana talakawa milyan 9 (9,458,160) gwannati ta shirya zasu samu wannan tallafi, daga gidaje fiye da miliyan 1, miliyan 5 yanzu sun fara samun tallafin a duk wata, wannan alkaluma sunzo ne a 31 ga Junairu 2020.

Ga alkaluma cikin hotuna kamar yadda hukumar NASSCO ta fitar a shafinta na Twitter .

Karin Labarai

UA-131299779-2