(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Abincin Korona: Kada ku karbi kayan sata da ‘ya’ya ko mazajenku suka kawo gida – Buhari

Karatun minti 1
Shugaba Buhari ya gaza
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya yi kira ga iyaye da kada su karbi kayan da ‘ya’yansu suka kawo wadanda suka balla rumbin abinci suka sato.

Kazakalika ya yi kira ga mata kan su tuhumi mazajensu kan kayan da suka shigo musu da shi gida.

Buhari ya bayyana haka ne sakamakon yadda fasa rumbin ajiye kayan tallafin Korona ya zama ruwan dare a wasu jihohin Najeriya.

Shugaban ya yi wannan kiran ne ta hannun hadiminsa, Mallam Garba Shehu cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog