Rahotanni daga birnin tarayyar Abuja, sun tabbatar da cewar wasu da ba a san ko suwaye ba sun fasa wani rumbum ajiyar Kayan Abincin Korona a garin.
Mutanen sun fasa rumbum dake a unguwar Idu kusa da tashar jirgin kasa, su ka kuma yi awon gaba da kayan abincin dake ciki.
DABO FM ta tattara cewar tin bayan fara farfasa rumbunan tallafin Kwabid-19 da wasu mutane suke yi a wasu jihohin Najeriya, an tsaurara matakan tsaro a rumbunan birnin na Abuja.
A kalla jihohi kusan 9 ne aka fasa rumbunan da aka ajiye tallafin Korona a ciki.
Jihohin sun hada da Adamawa, Edo, Ekiti, Osun, Ogun, Kaduna, Lagos, Pilatu da jihar Taraba.