(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Al’ummar Adamawa sun fasa rumbin ajiyar abincin tallafin Kwabid-19

Karatun minti 1

Jihar Adamawa ta biyo sahun wasu jihohin Najeriya da ‘yan jihar suke fasa ma’ajiyar abincin tallafin Kwabid-19.

DABO FM ta tattara cewa al’ummar afka wa ma’aijiyar abincin da safiyar yau Lahadi da karfe kusan karfe 11:20 a ma’ajiyar abincin dake Kwana-Waya a garin Adamawa.

Wasu bidiyoyin sun yi ta yawo na wasu mutane da suka gano inda abincin yake, sun kira ga sauran al’ummar garin da su zo su dauki kayayyakin.

A wani bidiyo da wani mai amfani da shafin Facebook, Mallam Rabiu Jalo ya nuna kai tsaye lokacin da al’amarin yake faruwa, ya nuna yadda mutane maza da mata suka rika wawason kayyakin.

An ga yadda mutanen suka rika daukar buhuhunan Shinkafa, kwalin Indomie da wasu kayayyakin abincin.

Jami’an tsaro sun isa wajen, sai dai sun kasa hana mutanen daukar kayan sakamakon yawansu.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta hannun kakakinta, DSP Sulaiman ta tabbatar da faruwar lamarin.

Zuwa yanzu al’ummar jihohin Ogun, Osun, Edo, Ekiti, Kwara, Kaduna, Lagos da Pilatou ne wawushe kayan abincin na tallafin Kwabid-19 da gwamnatocin jihar basu raba ba.

Tin bayan fara faruwar lamarin al’umma da yawa suna ganin cewar za a samu irin wadannan kayan abinci a kowacce jiha dake fadin Najeriya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog