Mutuwar Zakzaki a hannun gwamnati ba za ta haifar da ‘da mai ido ba – IMN

Karatun minti 1

Kungiyar Islamic Movement of Nigeria masu bin Shi’anci a Najeriya ta bayyana cewa mutuwar shugabanta a hannu gwamnati ba za ta haifar da ‘da mai ido ba.

Hakan na zuwa ne bayan wasu jita-jita da aka yi ta yadawa kan cewa shugaban IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya rasu.

Sai dai kungiyar ta ce labarin karya ne, shugaban yana nan da rai da lafiya, kamar yadda wani jigon kungiyar, Abdullahi Usman ya sanar.

Haka zalika a yayin tattaunawarsa da sashin Hausa na Jaridar Legit.ng, Abdullahi Usman ya ce mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati ba abu ne da zai zama mai alheri ba.

“Ban san daga inda mutane suka jiyo wannan jita-jitar ba, amma ina tabbatar maka cewa shugaban mu yana nan da ransa. Ba zai haifar wa gwamnati da mai ido ba idan shugabanmu ya mutu a hannunta,” ya kara da cewa.

Zuwa yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita a kafatanin kananun hukumomin jihar Kaduna wanda ba a san dalilan da ya sa aka sanya ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog