Gwamnatin Zamfara ta fara rabon Kayan abincin Kwabid-19, rigakafin ‘wawason’ al’umma

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Zamfara da Gwamna Bello Muhammad Matawalle yake jagoranta ta fara rarraba kayan abinci na tallafin Korona a jihar, a yau Lahadi, DABO FM ta tabbatar.

Hakan na zuwa ne bayan da al’ummar wasu jihohi a Najeriya suke farfasa ma’ajiyar Kayan Abincin suna dauka. An fasa a jihohin Adamawa, Ekiti, Edo, Osun, Ogun, Lagos, Kaduna da jihar Filato.

DABO FM ta tattara cewar da ranar yau Lahadi, gwamnatin jihar Zamfara bisa jagorancin babbar mai bai wa gwamna shawara kan ayyukan jinkai, Hon Faika Marshal M. Ahmad, ta raba kayan abincin a karamar hukumar Bungudu.

Yadda aka rarraba tallafin abinci a Bungudu, Zamfara

Wakilin mu ya hada mana cewa kayan sun hada da Shinkafa, Masara, Dawa, Taliyar Indomie, Makaroni da sauran kayan abinci.

Masu bukata ta musamman, mata da tsofaffi ne a yankin suka amfana daga rabon kayan abincin.

Sai ana ganin fargabar kada a fasa rumbum kayan abincin ne ya sa gwamnatin a yanzu ta dauki damarar rarraba kayan tallafin.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog