(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

An fara mayar wa Malamai kudaden da Ali Baba Agama Lafiya ya ‘zaftare’ musu

Karatun minti 1

Hukumar karfe korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta fara mayar wa da malaman da mai bawa gwamna shawara kan harkokin addinai ya zaftare musu na addu’ar Korona.

An dai zargi Ali Baba da yin zamba cikin aminci na karbewa malamai N45,000 daga N50,000 da gwamna Ganduje ya sahale a basu.

Da yake tabbatar da al’amarin, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da jihar Kano, Bar Muhiyi, ya shaida cewar tini hukumar ta fara bincike tare da fara mayar wa malaman da aka karbe kudin hakkokinsu.

A wani faifan bidiyo da hukumar ta dora a shafinta na Facebook, an hangi shugaban kungiyar tare da wadansu malaman da suka neman hakkokinsu da aka danne.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog