/

Ranar Matasa: ‘Ya kamata Gwamnati ta rika baiwa matasa fifiko a dukkanin lamuran ta’

dakikun karantawa

An yi kira ga matasa su cigaba da yin duk mai yiwuwa da bayar da gudunmuwar su wurin cigaban kasar da lalubo hanyoyin magance duk wasu matsalolin da ke damun al’umma.

Shugaban wata gidauniya ta Arewa mai rajin kare hakkin matasa da sanya su kan tsari wato Arewa Youth Trust Foundation a turance Ambasada Dakta Fahad Ahmad Chikaji, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Kungiyar ta fitar kan ranar tunawa da matasa ta duniya. da majalisar dinkin duniya ta ware 12 ga watan Ogusta na kowacce shekara. Taken ranar na bana shi ne, “Matasa su cigaba da sadukar da kan su domin fuskantar kalubalen zamani”.

Ya shawarci matasa su yi amfani da tanbihin wannan rana domin sanin ina suka dosa wurin gina rayuwar al’umma a matakai daban-daban.
A matsayin matasa na kashin bayan cigaban kowacce al’umma, a cewar sanarwar akwai bukatar matasa su kara zage damtse wurin shiga ana damawa da su a harkokin rayuwa ta kowacce fuska.

Ya shawarci gwamanatoci a kowanne mataki su rika baiwa matasa fifiko a dukkanin lamuran su, musamman a bangaren Ilimi da samar masu da aikin yi domin gina rayuwar su kamar yadda ta dace.

Ambasada Fahad Chikaji, ya kuma yaba ma gwamantin tarayya saboda samar da shirin tallafawa matasa na kasa wato N-Power da sauran shirye-shiryen tallafawa matasa da abubuwan dogaro da kai.

Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware duk ranar 12 ga watan Ogusta na kowacce shekara domin tunawa da matasa da kuma nazari a kan gudunmuwar da su ke bayarwa domin cigaban kasa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog