(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

‘An kama mutum 9 da ake zargi da kashe shugaban APC a jihar Nassarawa’

Karatun minti 1
Babban Sifetan 'Yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu

Gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa an kama mutum 9 da ake zarginsu da hannu kan sace wa da kuma kashe shugaban APC na jihar, Mista Phillip Tatari Shekwo.

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Juma’a ya yin da shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar da ke Lafia.

Ya ce an samu nasarar kama mutanen bayan da gamayyar jami’an tsaro suka gudanar da sumame inda ya kara da cewa tuni aka mika mutanen zuwa wajen ‘yan sanda domin bincike.

Rahotannin sun ce tun tuni aka binne sauran jikin shugaban jami’iyyar da aka samu.

A nashi bangaren, gwamna Abdullahi Sule ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba har sai an yi adalci kan kisan.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog