An yi garkuwa da a kalla mutum 1,570 cikin watanni 11 a Najeriya

dakikun karantawa
"Yan BIndiga

A kalla mutum 1,570 ne a ka yi garkuwa da su a Najeriya cikin kankanin lokacin da bai wuce watanni 11 ba, binciken Jaridar Daily Trust ne ya tabbatar da haka.

Kazalika, binciken ya ce masu garkuwa da mutanen sun iya samun Naira miliyan 311 daga cikin biliyan 6.9 da suka nema a matsayin kudin fansa  daga ‘yan uwan wadanda su ka yin garkuwar da su.

Binciken ya ce lissafin kudi babu na ‘yan uwan da suka biya miliyoyin kudi amma basa so a sani domin suna ganin za su fi samun kwanciyar hankali.

Daily Trust ta ce a abin ya yi tsananin da a  iya watan Nuwamba, an samu rahotanni da suka tabbatar da sace mutum 41. Daga cikin rahotan da ya fi daukar hankali har da wanda masu garkuwar suka shiga makarantar gaba da sakandire a jihar Kaduna.

A babban birnin tarayya kuwa, an samu rahotannin tabbatar sace mutune har guda 31 a watanni 11.

Daga cikin wuraren da ayyukan sace-sacen mutane suka ta’azzara sun hada da Titin Kaduna zuwa Abuja da Abuja zuwa Lokoja, inda nan za a iya cewa shi ne wajen cin karen masu garkuwa da mutane.

Ta’asar satar mutane ba ta kyale kowa a Najeriya ba, manya da yara, jami’an tsaro da wasu masu madafun iko a jami’iyun siyasar Najeriya.

Daga kan wani yaro dan shekara 7 da aka dauke a jihar Katsina wanda aka bukaci kudin fansa har Naira miliyan 3 zuwa ga wata dattijuwa ‘yar shekara 60 da aka sace a jihar Nijer, binciken ya ce ‘yan Najeriya sun shiga cikin halin matsananciyar fargaba.

Jami’an tsaro suma basu tsira daga ayyukan ta’addanci a Najeriya ba, domin a cikin watannin nan. Kwannan aka dauke Mataimakan Sufuritandan ‘yan sanda guda 12, Jami’an Kare hadura a titunan Najeriya, FRSC guda 10 , Jami’an Civil Defence 4 duk sun shiga hannun masu garkuwa da mutane. Abin ya yi munin da jami’an tsaro na farin kaya ma basu tsira ba, domin a watan Satumba, an dauke jami’inta.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Kungiyar Dattawan Arewa, da Gwamnonin yankin arewa maso gabas, da wasu kungiyoyi a Najeriya sun bayyana nasu irin bakin cikin game da halin da ‘yan Najeriya suka tsinci kansu sakamakon ayyukan satar mutane a Najeriya musamman arewacin kasar.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog