Tin da ba kwa so mazajenku su aure mu, za mu rika kai su dare in sun zo zance wajenmu – Wata Budurwa ta bayyana

Karatun minti 1

Wata mai amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya, Aisha Adam Gimbiya ta yi wani kira mai kama da kashedi kan cewa za su rika tsayar da masu zuwa zance wajensu har dare domin hukunta matan mazajen da suka hana su kara aure.

Aisha Adam Gimbiya, ita ce ta bayyana wannan ra’ayin nata a kafar Facebook a ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwambar 2020.

Ta ce; “Hmm… Ba dai kun ki bari su auro mu ba. To wallahi mu ma ba za mu dinga bari su dawo gida da wuri ba.”

Zancen ya janyo cece-kuce inda ya sha martanin nuna rashin so musamman daga matan aure, ya yin da a gefe guda kuma, wasu maza sun nuna jin dadinsu ga kalaman Aisha a kan wajen bayyana ra’ayinta na Facebook.

Wata mai suna Haufa Yusuf, ta ce; “Mace ai bata isa ta hana namiji kara aure ba sai dai ya miki karya ya ce miki matarshi ta hana shi. Ku cigaba da hanasu dawowa da wuri, yau gareka ne gobe ga ‘dan uwanka.”

Ita kuwa Sa’adatu Yunusa cewa ta yi; Tabbas wannan haka yake ‘yar uwa.

Daga bangaren maza kuwa, Aisha Adam Gimbiya yabo kadai take sha daga wajen maza. Muhammad Bello Abubakar yace; Kuma fa kin yi magana. Kwamared Sani Musa kuwa cewa ya yi; Kuma fa kin yi gaskiya.”

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog