(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

An nemi kotu ta dakatar da Hon Femi Gbajabiamila bisa laifin yin zambar dala 25,000 a Amurka

Karatun minti 1

Wani dan Najeria, Philip Undie, ya shigar da kokenshi zuwa ga wata babbar kotun tarayya dake Abuja, inda ya nemi kotun ta dakatar da Hon Femi Gbajabiamila dake zama dan majalissar wakilai bisa lafin zambar kudade da ya taba aikawa a kasar Amurka.


Koken da lauyan Mr Philipya shigar yace Gbajabiamila ya kamaci tsayawa takarar majalissar wakilai ba saboda an taba kama shi da laifin yin zamba da laifi mai kama da damfara a kasar Amurka.


Ya bayyana cewa an kama Gbajabiamila da laifin cutar wani mutum a Amurka dala 25,000, wanda yace hakan ya sabawa “Sashi na 66(1)(C) da (D) na cikin kudin tsarin mulki na shekarar 1999.


“Kasar mu bazata bawa wani damar zama kakakin majalissar tarayya ba, wanda ya kasance akwai laifi ko ayar tambaya akanshi ba.”
Har yanzu dai kotun bata saka ranar da za’a fara sauraren karar ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog