Ana ta Rai…: Majalissa dokoki ta aminta da karin sabbin masarautu a jihar Zamfara

dakikun karantawa

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zartar da kudirin neman kirkirar sabuwar masarauta a jihar.

A ranar Laraba ne majalisar ta amince da kudirin da aka gabatar a gaban ta na neman kirkirar sabuwar masarautar Bazai.


Ranar Laraba, majalissar jihar Zamfara dai ta amince da kudirin da aka gabatar a gabanta na neman kirkiran sabuwar masarautar Bazai tare da daga darajar hakimin Jangeru zuwa sarki yanka.


Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya rawaito cewa; Ibrahim Kwatarkwashi, dan majalissa mai wakiltar Bungudu ta Gabas, ya bawa majalissar rahoton kwamitin da aka nada na neman kirkirar masarautun da sarakunan ta a ranar Talata.


DaboFM ta tattaro cewa, bisa aminta da sabuwar masarautar da majalissar tayi, jihar Zamfara tanada Masarautu guda 18.


Shashin HAusa na Legit ya rawaito; “Kudirin ya samu tsallake karatu na biyu da na uku a zauren majalisar bayan Abubakar Gumi, mataimakin shugaban majalisar, ya karanta wa mambobin majalisar.


An kirkiri sabuwar Bazai ne daga masarautar Shinkafi. A cewar dokar da majalisar ta zartar, za’ a daga darajar babban hakimin Jangeru a masarautar Shinkafi zuwa sarkin Yanka mai daraja ta uku, yayin da za daga darajar Kayayen Marafa zuwa hakimi a masarautar Talata-Mafara.


Gumi ya bawa magatakardar majalisa umarnin ya sanar da bangaren zartarwa domin gaggauta a hannu a kan dokar.”

Duba irin tashe-tashen hankula da ake fama dasu a jihar Zamfara, ya dace a kirkiri sabbin masarautun?

Zaku iya bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na facebook, DABO FM.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog