(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ban taba samun matsala da Buhari ba – Shekarau

Karatun minti 1

Tsohon gwaman jihar Kano kuma dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jami’iyyar APC, Mal Ibrahim Shekarau yace, babu abinda ya taba shiga tsakaninshi da shugaba Muhammadu Buhari.

Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manewa labarai a gidanshi dake mundubawa a jihar Kano.

Shekarau, wanda ya kasance tsohon mai hamayyar da gwamantin shugaba Buhari kafin komawarshi jami’iyyar APC a shekarar data gabata.

Rabuwar Shekarau da Buhari ta samo asaline a shekarar 2011, lokacin da Shekarau ya nemi tsayawa takarar shugabanci Najeriya karkashin inuwar jami’iyyar ANPP. Masana na ganin Shekarau yayi amfani da karfin mulki wajen samun zama dan takara a jami’iyyar ANPP wanda hakan ya tilastawa Shugaba Buhari ficewa daga jami’iyyar ANPP zuwa jam’iyyar CPC mai alkalami.

Sai dai har ila yau ba’a taba ji inda shugaba Buhari ko Shekarau suka bada cikakken bayanai akan abinda ya kawo rabuwar kansu tin bayan haduwarsu a shekarar 2002.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog